Isa ga babban shafi

Birtaniya ta dakatar da daukar ma'aikatan lafiya daga Najeriya aiki

Birtaniya ta sanya Najeriya da wasu kasashe 53, cikin jerin kasashen da ba za ta rinka daukar ma’aikatan lafiya daga cikin su ba, bayan sauya ka’idojin daukar aiki ma’aikatan lafiya a kasar. 

Wasu ma'aikatan jinya a Najeriya
Wasu ma'aikatan jinya a Najeriya © KOLA SULAIMON/AFP
Talla

A sanarwar da ke dauke da sabbin ka’idojin, ta shawarci hukumomin da cibiyoyin da ke daukar ma’aikatan lafiya su kiyaye kasashen da ke cikin wancan jeri a lokacin daukar ma’aikatan lafiya. 

Wannan sabon tsarin dai ya shafi dukkanin ma’aikatan lafiya da za’a dauka aikin dindindin da kuma na wucin gadi a Birtaniya, wanda ya shafi likitoci da likitocin hakora da jami’an kimiyar lafiya da unguwar zoma da jami’an jinya da dai sauran su. 

Idan dai ba’a manta ba a shekarar 2021 ce, Ingila ta dakatar da daukar ma’aikatan lafiya daga Najriya da wasu kasashe 46, sabida barazanar kaura da kanana da matsakaitan kasashe ke fuskanta na karancin jami’an kiwon lafiya. 

A ranar 8 ga watan Maris da ya gabata kuma hukumar lafiya ta duniya WHO ta lissafa Najeriya da wasu kasashe 54 da ke fuskantar karancin jami’an kiwon lafiya. 

Rahotanni sun nuna cewar akwai kwararrun likitocin Najeriya dubu 11 da 55 da ke aiki a Ingila a yanzu haka, wanda hakan ya sanya kasar zama kasa ta uku da tafi yawan likitocin da ke aiki a kasar Ingila bayan India da Pakistan. 

Kasashen da wannan sabon tsarin ya shafa sun hada da Afghanistan, Angola, Bangladesh, Benin, Burkina Faso, Burundi, Cameroon, Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, Chadi, Comoros, Congo, Jamhuriyar Dimukaradiyar Congo, Cote d’Ivoire, Djibouti, Equatorial Guinea, Eritrea, Ethiopia, Gabon, Gambia, Ghana, Guinea, Guinea-Bissau, Haiti, Kiribati, Jamhuriyar Dimukaradiyar, Lesotho, Liberia. 

Sauran su ne Madagascar, Malawi, Mali, Mauritania, Tarayyar Micronesia, Mozambique, Niger, Nigeria, Pakistan, Papua New Guinea, Rwanda, Samoa, Senegal, Sierra Leone, Solomon Islands, Somalia, Sudan ta Kudu, Sudan, Tanzania, Timor-Leste, Togo, Tuvalu, Uganda, Vanuatu, Yemen, Zambia, da kuma Zimbabwe. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.