Isa ga babban shafi

Mutanen da aka halaka a Kakura ba 'yan bindiga bane - 'Yan sanda

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kaduna da ke Najeriya ta ce mutanen da aka nuna cewar an kama tare da halaka su a karamar hukumar Chikun cikin wani faifan bidiyo da ya yadu a baya bayan nan, ba ‘yan bindiga bane kamar yadda aka zarga.

Taswirar Najeriya da ke nuna jihar Kaduna.
Taswirar Najeriya da ke nuna jihar Kaduna. © Wikimedia Commons
Talla

Kwamishinan ‘yan sanda a jihar ta Kaduna Yekini Ayoku ne ya tabbatar da hakan, bayan jagorantar wani taron zaman lafiya da aka yi a ranar Litinin tsakanin al’ummar Gbagyi da Fulani a yankin Kakura.

A karshen makon da ya gabata wani faifan bidiyo ya bayyana a shafukan sada zumunta inda aka ga jami’an soji na tura wasu mutane da ake zargin ‘yan fashi ne cikin motar daukar kaya, da zummar zuwa wani asibiti a Kaduna.

Yayin da yake karin bayani kan lamarin, shugaban karamar hukumar Chikun Injiniya Salasi Nuhu Musa ya shaidawa sashin Hausa na RFI cewar suna samun labarin abinda ya faru na rasa rayukan da aka yi daga bangaren Gbagyi da Fulani suka guanar da binciken da ya gano cewar wadanda ake zargi da zama ‘yan fashin daji ne, an yi kuskure wajen tuhumar da aka yi musu.

00:41

Shugaban karamar hukumar Chikun kan mutanen da aka kashe bisa zarginsu da zama 'yan bindiga

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.