Isa ga babban shafi

Manajan bankin da aka sace ya biya naira miliyan 100 kafin sakinsa

‘Yan bindigar da suka kai hari kan jirgin kasan dake zirga zirga tsakanin Abuja zuwa Kadunan Najeriya sun karbi diyyar naira miliyan 100 kafin sakin shugaban bankin kula da ayyukan noma na kasar Alwan Hassan bayan ya kwashe kwanaki kusan 10 a hannunsu.

Shugaban bankin kula da ayyukan noma na Najeriya Alwan Ali Hassan
Shugaban bankin kula da ayyukan noma na Najeriya Alwan Ali Hassan © Daily Trust
Talla

Jaridar Daily Nigerian da ake wallafawa a kasar tace sabanin faifan bidiyon da ‘Yan bindigar suka gabatar cewar sun saki Hassan ne saboda yawan shekarun sa da kuma azumin watan Ramadan, wata majiya kusa da iyalan sa ta tabbatar da cewar sanda suka karbi makudan kudin kafin sakin sa.

Jaridar ta ce ‘Yan bindigar sun aike da sakon bidiyo ga iyalan Manajan Bankin inda suka bukaci a kaimu musu kudin ko kuma su hallaka shi, abinda ya sa iyalan suka kai musu kudin a wani dajin Jihar Kaduna, domin kubutar da shi.

Majiyar ta shaidawa Jaridar cewar da farko an umurci iyalan da su kai kudin wani daji dake Jihar Katsina, amma kuma daga bisani sai akace musu su koma Jihar Kaduna, inda suka cimma tarin ‘Yan bindigar dauke da makamai a wani daji, suka kuma mika musu makudan kudin.

'Yan bindiga sun yi ikirarin rashin karbar kudin fansa 

Faifan bidiyon da ‘Yan bindigar suka gabatar na nuna cewar su basu karbi ko kwabo ba daga hannun Manajan bankin kuma sun sake shi ne saboda yawan shekarunsa, inda suka bukaci gwamnatin Najeriya da ta biya musu bukatun su ko kuma su hallaka tarin fasinjojin dake hannun su yanzu haka.

‘Yan bindigar wadanda suka rufe fuskokin su a bidiyon da suka gabatar dauke da manyan bindigogi, sun ce ita gwamnati ta san bukatun su, saboda haka suna jiranta, kuma idan ta gaza zasu hallaka fasinjojin da suka kama.

Hukumar kula da sufurin jiragen kasa a Najeriya tace akalla fasinjoji sama da 140 ba’a iya ganin su ba bayan kazamin harin da aka kaiwa jirgin da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris, yayin da wasu majiyoyi ke cewa wadanda suka bata sun zarce wannan adadi ganin yawan mutanen dake neman ‘yan uwan su da suka bata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.