Isa ga babban shafi

Malaman Addini sun bukaci a yi wa 'yan ta'adda ruwan bama-bamai

Wata tawagar Fastoci dake karkashin wata kungiyar mabiya addinin Kirista ta 'United for Change Association', ta roki gwamnatin Najeriya da kuma rundunonin sojin kasar da su kaddamar da gagarumin farmaki kan ‘yan bindigar da suka addabi mutane, ta hanyar yi musu ruwan bama-bamai a cikin dazukan da suke boye a yankunan arewa maso yammaci, jihar Neja da kuma sauran yankin arewa ta tsakiya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, yayin duba faretin sojojin kasar a garin Dansadau, dake jihar Zamfara. 13/7/2016.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, yayin duba faretin sojojin kasar a garin Dansadau, dake jihar Zamfara. 13/7/2016. STRINGER / AFP
Talla

Limaman Cocin sun kuma roki shugaban Najeriya Muhd Buhari da yayi amfani da matsayinsa na babban kwamandan daukacin rundunonin tsaron kasar, y aba da umarnin fara amfani da sabbin jiragen yaki na zamani kirar Super Tucano da gwamnatinsa ta sayo daga Turai, domin murkushe ‘yan ta’addan kowa ma ya huta.

Shugaban kungiyar Fastocin David Adeniran ne yayi wannan kira, yayin taron nemana labarai da ya gudanar a garin Kaduna, inda yayi kira da al’ummar Musulmi da ma Kiristoci da su yi amfani da lokacin watan Ramadan wajen yawaita addu’o’in neman samun zaman lafiya.

Karuwar ta’addancin na 'yan bindiga da ake fuskanta a baya bayan nan ne ya sanya gwamnonin wasu daga cikin jihohin arewacin Najeriya, suka ce a shirye suke su nemo sojin haya domin kare rayuka da kuma dukiyoyin al’umma, matukar dai matsalar ta ci gaba da ta’azzara.

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-rufai, wanda ya zanta da wakilinmu Muhammad Kabiru Yusuf bayan da ya gana da shugaban kasar Muhammadu Buhari a cikin makon da ya gabata, inda ya ce babban abin takaici shi ne yadda jami’an tsaro suka gaza daukar matakin murkushe ‘yan bindigar duk da cewa ana da cikakkun bayanai a game da maboyarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.