Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun yi barazanar kashe fasinjojin jirgin kasan da suka sace

‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da fasinjoji da dama wadanda suka sace bayan harin da suka kaiwa jirgin kasan da ke kan hanyar zuwa Kaduna daga birnin Abuja a Najeriya, sun yi barazanar kashe dukkanin mutanen dake tsare a hannunsu idan gwamnatin Najeriya ta kasa biya musu bukatunsu.

Yan bindiga a Najeriya
Yan bindiga a Najeriya © Daily Trust
Talla

‘Yan bindigar sun yi barazanar ce a cikin wani faifan bidiyo da suka fitar a ranar Larabar da ta gabata, inda suka ce ba sa sha’awar a biya su kudi, sai dai gwamnati ta biya musu bukatun da suke nema, bukatun da ‘yan ta’addan suka yi ikirarin gwamnati ta san su.

Bidiyon, wanda bai kai minti biyu ba, ya nuna hudu daga cikin ‘yan fashin dajin tare da daya daga cikin fasinjojin da suka sace Alwan Hassan, wanda Manajan Darakta ne na Bankin Noma a Najeriya.

Daya daga cikin ‘yan bindigar da yayi magana da harshen Hausa ya ce an sako Manajan ne a dalilin tausaya masa saboda shekarunsa da kuma watan Ramadan.

Wani abu da ya dauki hankali a faifan bidiyon da ‘yan bindigar suka fitar shi ne yadda aka ga daya daga cikin motoci masu sulken da suka kona a farkon makon nan, yayin fafatawar da suka da sojojin Najeriya a Birnin Gwari dake Kaduna, abinda ke nufin an nadi bidiyon ne a sansanin sojoji na Polwire a garin na Birnin Gwari wanda aka kai wa hari ranar Litinin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.