Yan bindiga sun sake sakin bidiyon fasinjojin jirgin kasan da suka sace
Yan bindigar da suka yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasar da suka tare tsakanin Abuja zuwa Kaduna sun sake sakin wani faifan bidiyo mai dauke da fasinjojin suna rokon gwamnati da ta biya musu bukata domin kubutar da su.
Wallafawa ranar:
Daga cikin wadanda suka yi jawabi a bidiyon mai dauke da Yan bindigar dake rataye da makamai a bayan fasinjojin, ta bayyana kan ta a matsayin dalibar Jami’ar Jihar Kaduna inda ta bukaci a taimaka wajen ceto su.
Wata kuma ta bayyana kan ta a matsayin Gladys Tony wadda take aiki a ma’aikatar tsaro, yayin da wasu kuma suke zazzaune a kasa, wasu kuma a kwance.
A cikin bidiyon farko da suka saki dai, 'yan bindigar sun yi barazanar kashe dukkanin mutanen dake tsare a hannunsu idan gwamnatin Najeriya ta kasa biya musu bukatunsu, wadanda suka ce ta san dasu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu