Isa ga babban shafi
Najeriya-'Yan bindiga

'Yan bindiga sun kashe mutane 50 a Kaduna

Kimanin mutane 50 ne ‘’yan bindiga suka harbe har lahira, suka kuma yi awon gaba da wasu da ba a san adadinsu ba a hare-haren da suka kai kauyuka 9 a karamar hukumar Giwa ta jihar kaduna a Najeriya.

Hoton 'yan bindiga domin misali.
Hoton 'yan bindiga domin misali. © India TV News / PTI
Talla

Jaridar ‘Daily Trust’ da ake wallafawa a Najeriya ta ruwaito wani dan sa-kai a kauyen Dillalai yana cewa ‘ya bindigar sun kuma kone gidaje, motoci da babura, kana suka yi awon gaba da shanu sama da 100.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalinge, ya ce har yanzu rundunar ba ta tantance ainihin adadin wadanda suka mutu a yayin mamayar ba.

Jalinge ya ce har yanzu suna jiran cikakken bayani a ka lamarin daga babbn jami’in ‘yan sandan yankin Giwa da kuma babban jami’in ‘ya sand mai kula da yankin Zaria gaba daya.

Kauyukan da wannan alkaba’i ya shafa dai sune  Dillalai, Zangon Tama, Kaya, Barebari, Anguwan Bakko, Gidan Alhajin Kida, Kadanya Durumi da sauransu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.