Isa ga babban shafi
Najeriya-'Yan bindiga

'Yan bindiga sun kashe malamin makaranta a Kaduna

‘Yan bindiga sun kashe wani malamin  makaranta tare da wasu mutane 4 a unguwar  Layin lasan ta karamar hukumar Birnin Gwari a jihar kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Hoto domin misali kan 'yan bindiga.
Hoto domin misali kan 'yan bindiga. © Depositphotos
Talla

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da kungiyar kyautata tsaro da shugabanci na gari ta Birnin gwari, wadda kuma ta samu sa hannun shugabanta Ibrahim Abubakar Nagwari.

Zalika rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun yi awon gaba da mutane 16 a Dogon Dawa, layin mahuta da kuma kauyukan Tabanni a gabashin karamar hukumar.

Sanarwar ta ce lamarin ya auku ne a mabanbantan  lokutaa  cikin kwanaki 4 da suka wuce, tana mai cewa an kashe Haruna Tanko, wanda malamin makaranta ne tare da wasu mutane 4.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.