Isa ga babban shafi
Najeriya - Kaduna

'Yan bindiga sun kashe mutane 9 a kananan hukumomin Kaduna 4

Gwamnatin Kaduna ta ce ‘yan bindiga sun kashe karin mutane 9 a wasu kananan hukumomin jihar guda hudu yayin wasu. hare-hare da suka kai a baya bayan nan.

Alamun 'yan bindiga masu garkuwa da mutane a Najeriya
Alamun 'yan bindiga masu garkuwa da mutane a Najeriya Daily Trust
Talla

Kwamishinan tsaron cikin gidan jihar ta Kaduna Samuel Aruwan ne ya bayyana haka, bayan samun rahotanni kan hare-haren daga rundunonin soji da ‘yan sanda, kamar yadda ya bayyana cikin wata sanarwa da ya fitar a Juma’ar nan.

Aruwan ya ce kananan hukumomin da suka fuskanci hare-haren ‘yan bindigar sun hada da Chikun, Zaria, Igabi da kuma Zangon Kataf.

Kwamishinan ya ce a karamar hukumar Chikun an kashe mutane uku ne a yankin hanyar da ta tashi daga Kaduna zuwa Birnin Gwari, sai kuma wani mutu 1 a cikin garin na Chikun.

A kauyen Sako da ke Zangon Kataf kuwa, mutane 2 ‘yan bindiga suka kashe, yayin da jami’an tsaro suka gano gawarwakin wasu mutane 2. A Zaria kuwa mutum 1 ‘yan ta’addan suka halaka a kauyen Saye, yayin harin da suka kai a baya bayan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.