Isa ga babban shafi
Kaduna-'Yan bindiga

'Yan bindiga na karbar dafaffen abinci a matsayin kudin fansa

Yanzu haka ‘yan bindiga a Karamar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna a Najeriya sun bukaci a rika ba su dafaffen abinci a matsayin kudin fansa kafin sakin mutanen da suka yi garkuwa da su.

Gwamnatin Kaduna ta dauki wasu tsauraran matakai domin yaki da 'yan bindiga.
Gwamnatin Kaduna ta dauki wasu tsauraran matakai domin yaki da 'yan bindiga. © dailypost
Talla

Rahotanni na cewa, ‘yan bindigar sun janye daga kaddamar da hare-hare kan garuruwan jihar tun bayan da gwamnatin ta haramta cin kasuwannin mako-mako a wani bangare na daukar matakin magance matsalar tsaro.

Daya daga cikin shugabannin matasan kauyukan Birnin Gwari Babangida Yaro ya shaida wa Jaridar Daily Trsut cewa, tun lokacin da gwamnati ta haramta cin kasuwannin, ‘yan bindigar ke neman a rika ba su dafaffen abinci a duk lokacin da suka sace mutun.

Yaro ya kara da cewa, matakin hana sayar da man fetur a yankin, shi ma ya taimaka wajen takaita zirga-zairga.

A cewarsa, an samu kwarya-kwaryar zaman lafiya a kauyukan Damari da Kuyello da Kutemashi saboda ‘yan bindigar sun daina kaddamar da farmaki, yayin da suka tare a daji suna kwace dafaffen abinci hatta daga hannun masu sayar da abinci.

Har ila yau, Yaro ya kara da cewa, a duk lokacin da ‘yan bindigar suka sace mutune biyu zuwa uku a gona, suna barin mutun guda domin karbo musu abinci daga hannun iyalan wadanda aka yi garkuwa da su a matsayin fansa, la’akari da cewa, babu hanyar sadarwar wayoyin hannu da aka katse.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.