Isa ga babban shafi
Najeriya-'Yan bindiga

Dalibai mata 4 na Kaduna sun shafe makonni 10 a hannun 'yan bindiga

Dalibai mata 4 na kwalejin koyon aikin jinya mai zaman kanta ta Asma’u College of Health Technology dake jihar Kaduna a Najeriya sun shafe makonni 10 a hannun ‘yan bindiga da suka yi awon gaba da su a kan hanyar Birnin Gwari.

'Yan bindiga sun addabi sassan jihar Kaduna ta Najeriya
'Yan bindiga sun addabi sassan jihar Kaduna ta Najeriya © dailypost
Talla

Biyu daga cikin daliban wadanda ‘yan uwan juna ne, su na hannun barayin dajin ne tun daga ranar 21 ga watan Disamban 2021, lokacin da ‘yan bindigar suka tare ayarin motocinsu a kan hanyarsu ta zuwa birnin Gwari don hutun Kiristimeti, duk kuwa da rakiyar da jami’an tsaro suka yi musu.

Jaridar ‘Daily Trust’ da ake wallafawa a Najeriya ta ruwaito cewa mahaifin dalibai matan, ‘yan uwan juna, Lawal Ado ya ce ‘yan bindigar sun bukaci a biya Naira miliyan 10 a kan kowace daliba, kudin da har yanzu suka gaza hadawa.

Malam Ado,  wanda yake cikin tashin hankali ya ce ya zuwa yanzu ya biya Naira dubu dari 7, tare da katin waya na dubu 10 amma har yanzu ba a saki ‘yayan nasa ba.

 Gwamnatin jihar Kaduna, karkashin jagorancin Malam Nasir El-Rufai dai ta ci gaba da jaddada kudirinta na kin biyan kudin fansa ga masu satar  mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.