Isa ga babban shafi
Najeriya-'Yan bindiga

Dakarun Najeriya sun kashe 'yan bindiga 55 a Kaduna

 A Najeriya, mayakan rundunar Operation Thunder Strike/Whirl Punch sun kashe ‘yan bindiga 55 a yankin Labi da ke kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari a jiya Alhamis.

Wasu sojojin Najeriya.
Wasu sojojin Najeriya. Pulse.ng
Talla

Daraktan yada labarai na ma’aikatar tsaron kasar, Manjo Janar Benard Onyeuko ne ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja.

Ya ce mayakan rundunar sun yi wa ‘yan bindigr dirar mikiya ta sama a yayin fafatawar, inda dakarunta suka dinga yi wa barayi daji bugun kwaf daya ta kasa.

‘Yan bindiga dai sun addabi al’umar yankuna da dama a yankin arewa maso yammacin Najeriya, inda suke satar dabbobi da kuma mutane.

Sau da dama wadannan barayi na dora wa garuruwan da hukumomin kasar suka gaza karewa haraji, wanda rashin biyan wannan haraji na iya janyo musu mummunan kisa.

A  cikin wannan makon, gwamnatin tarayar Najeriya da na jihohi sun bayyana shirin hada karfi da karfe wajen yakar wadannan ‘yan bindiga da ke cin zarafin al’umma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.