Isa ga babban shafi
Kaduna-'Yan bindiga

Al'ummomi sama da 100 ne suka tsere daga garuruwansu a Kaduna

A Najeriya sama da al’ummomi 100 ne suka tsere daga garuruwansu sakamakon ayyukan ‘yan bindiga da kuma rikice rikicen addini da kabilanci da ya hada da rikicin manoma da makiyaya  a jihar Kaduna.

'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya
'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya © dailypost
Talla

Wani rahoton da jaridar ‘Daily Trust’ ta wallafa ya gano garuruwa 143 a kananan hukumomin Zangon Kataf, Kauru, Birnin Gwari, Chikun, Giwa, Igabi da Kajuru, da ‘yan bindiga suka daidaita al’ummominsu.

Da take  tabbatar da wadannan alkalumman daga Birnin Gwari, kungiyar tabbatar da ci gaban masarautar Birnin Gwari ta ce a karamar hukumar kawai, akwai kauyuka 60 da ‘yan bindiga suka kori al’ummominsu tun ashekarar 2021.

Shugaban kungiyar, Haruna Salisu, wanda lauya ne, ya ce babu wai mahaluki da ke zaune a wadannan kauyuka, yana mai  cewa mutanen yankunan wadanda manoma  ne sun bar mahaifarsu ba don sun so ba, amma saboda cin zarafin da ‘yan bindiga ke musu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.