Isa ga babban shafi
Najeriya-Kaduna

Kaduna ta sanya dokar hana fita a kananan hukumomin Kaura da Jama'a

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanya dokar hana fita ta sa’o’I 24 a kananan hukumomin Jama’a da Kaura a wani yunkuri na kwantar da hankulan jama’a biyo bayan tarzomar da ta hallaka mutane da dama.

Kwamitin tsaro na jihar Kaduna a Najeriya.
Kwamitin tsaro na jihar Kaduna a Najeriya. © Kaduna State Government
Talla

Kwamishinan tsaron cikin gida Samuel Aruwan ya ce matakin ya biyo bayan shawarwarin masana tsaro biyo bayan tarzomar.

Aruwan ya shaidawa manema labarai cewa, jami’an tsaro za su tabbatar da doka da oda a yankunan da tarzomar ta faru.

Rahotanni sun ce tun farko wasu fusatattun matasa ne suka farwa matafiya bayan kisan wani magidanci a Kafanchan.

Gwamnatin jihar ta Kaduna ta baki Samuel Aruwan ya roki al’umma su bi umarnin don tabbatar da tsaro da rayukan al’umma a kananan hukumomin biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.