Isa ga babban shafi
Najeriya - Kaduna

'Yan bindiga sun saki mambobin Cocin Baptist fiye da 60 a Kaduna

‘Yan bindiga sun saki mambobin Cocin Baptist 61 dake Kakau Daji a Kaduna bayan shafe wata daya suna garkuwa da su.

Wata uwa rungume da diyarta bayan da 'yan bindiga suka sake ta tare da dalibai da dama daga wata makaranta a Kaduna, a ranar 25 ga Yuli, 2021.
Wata uwa rungume da diyarta bayan da 'yan bindiga suka sake ta tare da dalibai da dama daga wata makaranta a Kaduna, a ranar 25 ga Yuli, 2021. - AFP/Archivos
Talla

Da yammacin ranar Juma’ar nan da ta gabata ne, shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya ta CAN reshen Jihar ta Kaduna, Joseph Hayab ya tabbatar da sako mutanen.

Yayin karin bayani a jiya Asabar Hayab y ace tun da farko sai da ‘yan bindigar suka nemi a basu kusan naira miliyan 100 kafin sakin wadanda suka yi garkuwar dasu, said ai bai yi karin bayan kan ko an biya kudaden ba.

A ranar 31 ga watan Oktoban da ya gabata, gungun ‘yan bindigar suka kai farmaki kan Cocin na Baptist dake karamar hukumar Chikun inda suka yin awon gaba da mutane 66, inda daga bisani suka kashe 2 daga cikinsu, wasu uku kuma suka sake su saboda rashin lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.