‘Yan bindiga sun saki karin daliban sakandaren Bethel Baptist
‘Yan bindiga sun saki karin dalibai 10 da suka sace daga makarantar sakandare ta Bethel Baptist da ke jihar Kaduna.
Wallafawa ranar:
Daliban sun sake samun 'yanci ne a jiya Asabar, bayan sun shafe kimanin kwanaki 75 a hannun ‘yan binidgar da suka yi garkuwa dasu.
An sace daliban ne dai tun ranar 5 ga watan Yuli lokacin da gungun ‘yan bindiga suka kaiwa makarantar ta Bethel Baptist farmaki a karamar hukumar Chikun da ke Kaduna.
Wani babban jami’I a makarantar ya shaidawa manema labarai cewa an saki daliban ne bayan biyan kudaden fansar da ba a bayyana adadinsu ba.
Karin daliban 10 da suka samu 'yanci, ya sanya a halin yanzu adadin wadanda ‘yan bindigar suka saki kaiwa 100 daga cikin 121 da suka sace a watan Yuli.
Da fari dai 'yan bindigar sun saki daliban 28 ne a ranar 25 ga watan Yuli, bayan da aka ce an biya su kudin fansa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu