Isa ga babban shafi
Najeriya - Kaduna

Dakarun Najeriya sun ceto jami'in da 'yan bindiga suka sace daga NDA

Dakarun Najeriya sun kubutar da hafsan sojin da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi a watan da ya gabata, bayan sa ce shi da suka yi daga babbar makarantar horas da soji ta NDA da ke jihar Kaduna.

Wasu sojojin Najeriya
Wasu sojojin Najeriya © Lekan Oyekanmi/AP
Talla

A ranar 24 ga watan Agustan da ya gabata, gungun ‘yan bindiga suka kai hari kan Kwalejin horas da Hafsoshin Sojin, inda suka kashe jami’ai guda 2 tare da yin garkuwa da wani.

Cikin sanarwar da ta fitar, rundunar sojin Najeriya ta ce, a ranar Juma’a dakarun ta suka kai samame kan sansanin da ake tsare da babban jami’in na ta a yankin Afaka da ke kusa da makarantar sojin.

Bayan fafatawa da 'yan bindigar ne kuma sojojin suka samu nasarar kubutar da jami'in.

Rundunar ta ce an lalata sansanonin 'yan bindigar da dama tare da kashe su yayin samamen.

Sojojin Najeriya yayin daukar horo.
Sojojin Najeriya yayin daukar horo. © Nigerian Defence Academy

Harin da aka kai wa makarantar ta NDA da ke horar da hafsoshin sojan Najeriya da na wasu kasashen Afirka, ya haifar da kaduwa tsakanin jama’a, duk da cewar mayakan da ke ikirarin jihadi a arewa maso gabashin kasar sun sha kaiwa sansanonin soji farmaki.

Yankin Arewa maso Yamma da Tsakiyar Najeriya dai na fama da ‘yan bindiga da ke kai hare -hare a kauyuka, suna kashewa tare da sace mutane da dabbobi gami da kona gidaje.

Makwanni biyu da suka gabata, sojojin Najeriya suka kaddamar da hare-hare ta sama da ta kasa kan sansanonin 'yan bindiga a jihar Zamfara, a yayin da aka katse layukan sadarwa, da nufin taimakawa jami’an tsaron wajen murkushe miyagun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.