Isa ga babban shafi
Najeriya

’Yan bindiga sun shafe kwanaki 4 suna tare hanyar Abuja zuwa Kaduna

Matsalar tsaro na cigaba da zama babban kalubalen dake addabar jama’a musamman a yankin arewacin Najeriya, la’akari da yadda ‘yan bindiga ke cigaba da kai hare-hare da sace mutane akai–akai, duk da kokarin kakkabe su da jami’an tsaro ke yi.

Wani bangare na babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Wani bangare na babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja. © Premium Times
Talla

A baya bayan nan dai sai da ‘yan bindigar suka datse babbar hanyar dake sada birnin Abuja da Kaduna har sau 4, daga ranar Lahadi zuwa Laraba, inda suka sace mutane da dama.

Hanyar ta Abuja zuwa Kaduna dai na da muhimmancin gaske ga matafiyan dake baluguro daga kudanci zuwa arewacin Najeriya.

Harin da ya fi muni dai shi ne na ranar lahadi wanda bayanai suka ce ‘yan bindigar sun sace matafiya da dama wadanda kawo yanzu ba a san adadinsu ba, zalika cikin mutanen da suka rasa rayukansu akwai tsohon dan takarar gwamna a jihar Zamfara Sagir Hamidu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.