Isa ga babban shafi
Najeriya - Kaduna

'Yan bindiga sun saki karin daliban Bethel Baptist 10

‘Yan bindiga sun saki karin dalibai 10 na makarantar bethel Baptist da suka sace a Kaduna.

Wasu iyayen daliban makarantar sakandaren Bethel Baptist a cikin harabar makarantar yayin da suke addu'ar dawowar yaransu a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya. Ranar 14 ga Yuli, 2021.
Wasu iyayen daliban makarantar sakandaren Bethel Baptist a cikin harabar makarantar yayin da suke addu'ar dawowar yaransu a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya. Ranar 14 ga Yuli, 2021. Kola Sulaimon AFP
Talla

Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya reshen jihar ta Kaduna Joseph Hayab, ya ce an saki daliban ne da yammacin ranar Lahadi, kuma tuni an sada su da iyayensu.

A watan Yulin da ya gabata 'yan bindiga suka yi awon gaba da dalibai 121, wadanda daga bisani suka rika sakin adadin yaran rukuni rukuni.

An dai sace daliban ne dai tun a ranar 5 ga watan na Yuli lokacin da gungun ‘yan bindigar suka kaiwa makarantar Bethel Baptist farmaki a karamar hukumar Chikun da ke Kaduna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.