Isa ga babban shafi
Najeriya - Kaduna

An dage zabe a kananan hukumomi hudu na Kaduna saboda rashin tsaro

Hukumar zabe mai zaman kanta a Kaduna, ta dage zabukan da aka shirya gudanarsu yau ranar Asabar na sabbin Shugabanni da kuma Kansiloli a wasu kananan Hukumomin jihar hudu.

Wani jami'in dan sanda a jihar Kaduna dake arewacin Najeriya.
Wani jami'in dan sanda a jihar Kaduna dake arewacin Najeriya. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Shugabar Hukumar zaben, Saratu Dikko Audu, ta ce matakin ya biyo bayan rahotannin yiwuwar fuskantar barazanar tsaro da ke cewa ba zai yiwu a gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali a wuraren ba.

Kananan hukumomin da dage zaben ya shafa dai sun hada da Birnin Gwari, Chikun, Zangon Kataf da kuma Kajuru.

An sauya ranakun zaben Shugabannin kananan hukumomin da Kansilolin zuwa ranar 25 ga watan Satumban da muke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.