Isa ga babban shafi
Najeriya-Kaduna

Mun shirya yin luguden wuta kan wadanda suka sace daliban Forestry -El -Rufai

Gwamnan Jihar Kaduna da ke Najeriya Malam Nasir El-Rufai ya ce gwamnatinsa ta shirya kai hari maboyar 'yan bindiga domin yi musu ruwan bama bamai ko da za’ayi asarar wasu daga cikin daliban jihar 27 na kwalejin Afaka da aka sake su.

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa'i
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa'i Twitter@GovKaduna
Talla

El-Rufai ya ce kashe wasu daga cikin daliban zai zama kuskure ne da ya ke shirye ya dauki nauyi maimakon biyan 'yan bindigar kudi a matsayin kudin fansa domin sakin daliban.

Gwamnan ya ce kwanaki biyu bayan sace daliban na Afaka, sojojin sama da na kasa sun shaida masa inda 'yan bindigar suke tare da daliban da kuma yadda suka musu kawanya.

El-Rufai ya ce sun shirya afka musu, ko da yake ya san cewar zasu rasa wasu daga cikin daliban, amma hakan zai bada damar kashe 'yan bindigar baki daya da ceto sauran daliban.

Jaridar Premium Times ta ruwaito Gwamnan na cewa ya san hadarin da ke tattare da kai harin da kuma sanin cewar ana iya kashe wasu daliban, amma hakan mataki ne mai kyau.

El-Rufai ya ce a irin wannan yaki dole ne wasu su sadaukar da rayukan su domin a samu nasara maimakon biyan kudi dan ganin an saki daliban.

A ranar larabar da ta gabata ne aka saki daliban 27 a karkashin wani shirin tattaunawa da Sheikh Ahmad Gumi da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo suka jagoran ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.