Isa ga babban shafi
Najeriya-Kaduna

'Yan bindiga sun saki bidiyon daliban da suka sace a Kaduna

'Yan bindigar da suka sace daliban kwalejin aikin noma da ke Jihar Kadunan Najeriya sun saki faifan bidiyo mai dauke da hotan wasu daliban suna rokon da a taimaka a cece su.

Jami'an tsaro a kofar makarantar horos da aikin noma, inda aka sace dalibai a Kaduna
Jami'an tsaro a kofar makarantar horos da aikin noma, inda aka sace dalibai a Kaduna Bosan Yakusak AFP/File
Talla

Bidiyon na dakikoki 56 da aka nada cikin dare ya nuna wani daga cikin 'yan bindigar na magana cikin harshen  Hausa da Fulatanci, inda ya bukaci daliban da su yi magana a gaban na’urar daukar hoto.

A cikin bidiyon, wata daga cikin daliban da ake kira Hajiya ta roki iyayensu da su taimaka su ceto su saboda sun gaji da zama a wurin da babu abinci.

Dalibar ta ce sun kwashe kwanaki 47 a hannun 'yan bindigar kuma da yawa daga cikinsu suna fama da rashin lafiya kuma ba sa samun abinci, yayin da suke kwana a filin Allah Ta'ala duk da ruwan sama da ake yi a wani lokaci.

'Yan bindigar sun kuma gabatar da wata mata da suka ce matar wani soja ne da suka kama a gidanta da ke Tirkania-Agwa da ke Karamar Hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Matar ta ce, mijinta sojam ruwa ne da ke aiki a Warri na jihar Delta, inda ta bukaci gwamnatin tarayya da ta kai musu dauki.

Matar ta ce 'yan bindigar sun bukaci Naira miliyan 30 a matsayin diyya kafin su sake su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.