Isa ga babban shafi
Kaduna-Najeriya

'Yan bindiga sun saki daliban jihar Kaduna 27 bayan watanni 2

Rahotanni dake shigo mana daga Najeriya sun nuna cewar Yan bindigar da suka sace dalibana kwalejin gandun dajin Jihar Kaduna 27 sun sake su yau Laraba.

Wani hoto domin misali dake nuna 'yan bindiga.
Wani hoto domin misali dake nuna 'yan bindiga. Getty Images/iStockphoto - zabelin
Talla

Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a Najeriyar tace kwamitin Sheikh Ahmad Gumi ne ya taimaka wajen kubutar da daliban wadanda suka kwashe kusan wata biyu a hannun wadanda suka sace su.

Daliban na daga cikin 37 da aka kwashe a makarantar, yayin da aka saki 10 daga cikin su bayan biyan diyya.

Gwamnatin Jihar Kaduna taki amincewa da bukatar Yan bindigar na biyan su naira miliyan 500 kafin sakin daliban abinda ya kaiga zaman su na dogon lokaci a hannun wadanda suka yi garkuwa da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.