Isa ga babban shafi
Najeriya - Kaduna

'Yan bindiga sun sake kai hari Kaduna tare da kashe akalla mutum biyu

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce wasu da ake zargin ’yan fashi ne sun kashe mutum biyu tare da raunata wasu maza shida a wasu hare-hare daban-daban da suka kai kananan hukumomin Chikun da Kajuru na jihar.

Hoton domin misali kan 'yan bindiga.
Hoton domin misali kan 'yan bindiga. © Depositphotos
Talla

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Talata a Kaduna.

Mista Aruwan ya ce jami'an tsaro sun ba da rahoton cewa 'yan bindiga sun mamaye Mazari, wani gari kusa da Buruku a karamar hukumar Chikun, mutum daya ya mutu a harin, sannan wasu uku sun jikkata.

Ya bayyana cewa a wani lamarin, yan fashin sun kai hari a kauyen Doka, karamar hukumar Kajuru, sun kashe mutum daya tare da raunata wasu uku.

Kaduna na daga cikin jihohi masu fama da rikici

Kaduna na daya daga cikin jihohin da ke fama da matsalar 'yan fashi a Najeriya. Daruruwan mutane ne 'yan fashi suka kashe ko suka yi garkuwa da su a cikin' yan shekarun nan.

Sauran jihohin da irin wannan ta'addancin ya shafa sun hada da Neja, Zamfara da Katsina.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.