Isa ga babban shafi

ICJ za ta yanke hukunci kan zargin Isra'ila da kisan kare dangi a Gaza a yau juma'a

A yau juma'a ake sa ran kotun Duniya a zaman ta na karshe za ta zartas da hukunci kan karar da Afrika ta kudu ta shigar gabanta wadda ke tuhumar Isra’ila da kisan kare dangi a Gaza bayan kashe tarin fararen hular da yawansu ya haura dubu 25 galibinsu mata da kananan yara daga ranar 8 ga watan Oktoba kawo yanzu.

Zaman kotun ICJ
Zaman kotun ICJ REUTERS - THILO SCHMUELGEN
Talla

Isra’ila dai na ci gaba musanta zargin baya ga kira ga kotun kan ta yi watsi da karar ta Afrika ta kudu bisa kafa hujja da cewa Hamas ta kashe mutanen da yawansu ya kai dubu 1 da 200 a hare-haren da ta kai mata ranar 7 ga watan Oktoba.

Yankin zirin Gaza
Yankin zirin Gaza © AFP

Gabanin zaman kotun na ICJ a yau, Majalisar Dinkin Duniya ta aike da tawagar kwararru yankin na Gaza don gudanar da cikakken bincike kan zargin kisan kare dangin na Isra’ila kan Falasdinawa.

Wasu daga cikin mutanen da harin Isra'ila ya ritsa da su  a Gaza
Wasu daga cikin mutanen da harin Isra'ila ya ritsa da su a Gaza AP - Hatem Ali

Babu dai tabbacin ko hukuncin kotun zai mara baya ga Afrika ta kudu da sauran kasashen da suka mara mata baya a hukuncin, sai dai bukatar wasu hujjoji masu zaman kansu da kotun ta yi a baya-bayan nan ya sanya shakkun yiwuwar Isra’ilan ta gaza tasiri wajen sauya hukuncin kotun.

  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.