Isa ga babban shafi

Afrika ta kudu ta bukaci ICJ ta dakatar da kisan kare dangin Isra'ila a Gaza

Kotun Duniya ta kammala sauraron hujjojin da Afrika ta kudu ta gabatar mata game da karar da ta shigar kan tuhumar Isra’ila da aikata kisan kare dangi a Gaza, inda yayin zaman shari'ar na yau Alhamis kasar ta kudanci Afrika da ke samun goyon bayan kasashe 5 a shari'ar ta bukaci kotun ta ICJ ta dakatar da Isra'ila daga kisan kare dangin da ta ke yiwa Falasdinawa a Gaza.

Zaman kotun ICJ yau Alhamis kan shari'ar da Afrika ta kudu ta shigar da ke tuhumar Isra'ila da kisan kare dangi a Gaza.
Zaman kotun ICJ yau Alhamis kan shari'ar da Afrika ta kudu ta shigar da ke tuhumar Isra'ila da kisan kare dangi a Gaza. REUTERS - THILO SCHMUELGEN
Talla

Tuni dai Isra’ila ta musanta dukkanin zarge-zargen bayan da Afrika ta kudu ta gabatar da hujjojin da ke tabbatar da kisan kare dangin da Sojojinta ke ci gaba da yi a Gaza da zuwa yanzu kasar ta Yahudawa ta kasha Falasdinawa fiye da dubu 23 baya ga rushe kashi 83 na gine-gine yankin.

Bayan da lauyoyi suka kammala gabatar da dukkanin hujjojin da Afrika ta kudu ta mika kan kisan kiyashin na Isra'ila a Gaza, bayanai na nuna cewa sai a nan gaba ne kotun ta ICJ za ta yi zama na musamman kan shari’ar.

Afrika ta kudu wadda ke da daddiyar dangata da yankin Falasdinu tun zamanin mulkin Nelson Mandela wanda ya ke matsayin aboki ga Yasser Arafat.

Tun a wancan zamani shugabannin biyu na kallon gwagwarmayarsu a matsayin tafiya guda lura da yadda Afrika ta kudu ke fafutukar ‘yancin bakar fata a hannu guda Falasdinu ke fafutuka kan mamayar da Isra’ila ke mata.

Fiye da shekaru 30 kenan Afrika ta kudu na nuna cikakken goyon baya ga yankin na Falasdinu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.