Isa ga babban shafi

Afrika ta Kudu ta maka Isra'ila a Kotun Duniya kan yakin Gaza

Kasar Afrika ta Kudu ta shigar da kara a gaban Kotun Duniya ta ICC, inda ta bukaci kotun da ta gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa Isra’ila na aikata laifukan yaki a Zirin Gaza.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu © Ohad Zwigenberg / AP
Talla

Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa ya sanar da wannan matakin da kasarsa ta dauka kan Isra’ila wanda ke zuwa a daidai lokacin da ‘yan majalisar kasar ke shirin tafka muhawara a wannan Alhamis kan yiwuwar rufe ofishin jakadancin Isra’ila da ke kasar ta Afrika ta Kudu.

Kazalika ‘yan majalisar na duba yiwuwar katse duk wata huldar diflomasiyya da Isra’ila har sai ta amince ta tsagaita bude wuta a Gaza.

Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa ya ce, sun yi amanna cewa, Isra'ila ta wuce makadi da rawa a Gaza.
Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa ya ce, sun yi amanna cewa, Isra'ila ta wuce makadi da rawa a Gaza. AP - Themba Hadebe

Shugaba Ramaphosa wanda ke magaba a Qatar ya bayyana cewa,  lallai kasarsa ta yi amanna cewa, Isra’ila ta aikata laifukan yaki tare da kisan kare dangi a Zirin Gaza, inda dubban Falasdinawa suka rasa rayukansu tare da ruguza asibitoci da kayayyakin more rayuwa na al’umma.

Kodayake shugaban na Afrika ta Kudu ya ce, ba su lamunci abin da mayakan Hamas suka aikata ba na kaddamar da farmaki kan Isra’ila da ya kashe Yahudawa akalla dubu 1 da 400.

Tuni dai jam’iyyar ANC mai mulki a Afrika ta Kudu ta bayyana cewa, za ta goyi bayan kudirin da ‘yan adawar kasar suka gabatar na ganin cewa kasar ta rufe ofishin jakadancin Isra’ila tare da katse duk wata huldar diflomasiyya da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.