Isa ga babban shafi
Australia-Tuvalu

Australia zata fara karbar yan gudun hijirar dumamar yanayi daga tsibirin Tuvalu

Kasar Australia ta bayyana aniyar karbar yan gudun hijirar dumamar yanayi daga tsibirin Tuvalu. A yau juma’a 10 ga watan Nowamba, Faraministan Australia Anthony Albanese ya bayyana cewa, kasashen biyu sun cimma yarjejeniya a tsakaninsu, da za ta bada damar karbar kimanin  yan gudun hijirar gurbacewar yanayin da ke zaune a tsibirin Tuvalu su kimanin dubu 11.200,  da su je su zauna a kasar ta Australia.

Wani ministan a tsibirin Tuvalu tsaye a daya daga cikin tsibaran da suka nutse a Tuvalu.
Wani ministan a tsibirin Tuvalu tsaye a daya daga cikin tsibaran da suka nutse a Tuvalu. via REUTERS - Tuvalu Foreign Ministry
Talla

Ana daukar tsibirin na Tavalu a matsayin kasar Farko da barazanar  matsalar  dumamar yanayi dake haddasa kara hauhawan ruwan teku, ke barazanar shafewa daga doron kasa. Za a iya cewa, wannan wani mataki ne mai muhimmanci da ba taba dauka ba,  Firaministan Australia Anthony Albanese ya sanar a yau juma’a 10 ga watan nowamba 2023.

Albarkacin ziyarar  aikin da ya kai a tsibirin Cook,  domin halartar zaman taron tsibiran da ke kan tekun  Pacifique, inda ya bayyana cewa sun saka hannu kan yarjejeniyar karbar yan gudun hijirar dumamar yanayi,   da tsibirin Tuvalu, da za ta bada damar karbar kimanin mutne dubu 11.200, da ke fuskantar gagarumar barazana kara hauhawar ruwan teku, su koma da zama a kasar  Australie. Za a kirkiro da wata sabuwar  takardar Visa ta musaman, domin  wadannan yan gudun hijira.

« Fara ministan Austaralia Anthony Albanese, ya ce, kasar Austarlia za ta samar da sabon tsari na musaman da zai bada damar karbar kimanin mutane 280 a kowace shekara. Hanyar da za ta baiwa mazauna tsibirin na Tubalu damar  zuwa kasar ta  australia su yi rayuwa, aiki ko kuma karatu» Tuni dai biyu daga cikin tsibirai 9, da suka hada tsibirin na Tuvalus sun nutse cikin ruwa,  haka kuma kwararun kan dumamar yanayi  sun bayyana cewa , gabadayan tsibiran za su karasa nutsewa ne a cikin shekaru 80 masu zuwa nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.