Isa ga babban shafi

An gano jirgin da Amurka ta nutsar dauke da 'yan Australia dubu a Yakin Duniya na 2

A yau Asabar masu binciken can cikin karkashin teku sun ce sun gano wani jirgin fasinjan Japan na lokacin yakin duniya na 2, wato Montevideo Maru, wanda aka nutsar da shi a tekun  Philippines  dauke da ‘yan Australia 1000.

Sojin ruwan Amurka ne suka nutsar da wannan jirgi mai suna Montevideo Maru, mallakin Japan a shekarar 1941.
Sojin ruwan Amurka ne suka nutsar da wannan jirgi mai suna Montevideo Maru, mallakin Japan a shekarar 1941. REUTERS/Nguyen Ha Minh
Talla

Jirgin ruwan yakin Amurka, wanda ma’aikatansa ba su ankare cewa jirgin na dauke da fursunonin yaki ne ya nutsar da wannan jirgi a ranar 1 ga watan Yulin shekarar 1942.

Kungiyar binciken tarihi na karkashin ruwa ta Silentworld, waddda ta dauki nauyin binciken ta ce an gano jirgin ne a waje mai nisan sama da kilomita 4 a karkashin tekun.mo

Nutsewar jirgin ruwan Montevideo Maru shine hatsarin jirgin ruwa mafi muni da kasar Australia ta fuskanta, inda ta yi asarar akalla mutane 979, cikinsu sojoji 850.

Fararen hula daga kasashe 13 na cikin wannan jirgi, abin daya kawo adadin fursunonin da suka mutu a ciki dubu 1 da 60.

Dakarun Japan ne suka kama su watannin baya kafin balaguron a garin gabar teku na Rabaaul a Papua New Guinea.

Bayan shafe shekaru 5 suna shiri, masu binciken sun fara aikin neman jirgin ne a ranar 6 ga watan  Afrilu  daga tekun kudancin China, arewa maso  yammacin tsibirin Luzon na Philippines.

Sun fara hangen nasara ce kwanaki 12 kacal bayan da suka kaddamar da neman jirgin ruwan, ta wajen amfani da na'urorin zamani har da motar karkashin ruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.