Isa ga babban shafi

Kamaru za ta fara ginin layin dogo zuwa Congo duk da takaddama da kamfanin Australia

Gwamnatin Kamaru ta sanar da shirin fara aikin ginin wani layin dogo da zai sada yankin nan mai albarkatun karafa da aka jima ana takaddama kansa daga iyakar kasar zuwa jamhuriyyar demokradiyyar Congo.

China ke shirin jagorantar aikin ginin layin dogon tare da hakar ma'adinan na tama da karafa akalla ton miliyan 35 duk shekara.
China ke shirin jagorantar aikin ginin layin dogon tare da hakar ma'adinan na tama da karafa akalla ton miliyan 35 duk shekara. 路透社照片
Talla

Ma’aikatar hakar albarkatu ta Kamaru ta ce wasu kamfanonin China 2 da ta kulla yarjejeniya da su tun a shekarar 2021 ne za su jagoranci aikin ginin, wanda za a fara a watan Agusta mai kamawa.

Sanar da aikin fara shimfida layin dogon dai na zuwa ne duk da yadda wani kamfanin Australia na Sundance Resourcesda tun farko ya kulla yarjejeniyar aikin ginin da kuma aikin kwasar albarkatun karafan, ya shigar da gwamnatocin kasashen biyu gaban kotun don kalubalantar hadakar ta su da China.

Tsawon lokaci aka shafe ana takaddama tsakanin gwamnatocin kasashen na Kamaru da Congo da kuma masu fafutukar kare muhalli wanda ya sanya kamfanin na Sundance Resources jinkirta aikin, dalilin da ya tilasta Kamaru juyawa ga China.

Tun a shekarar 2021 ne Kamaru ta sanya hannu kan yarjejeniya tsakaninta da masu zuba jari na China wadda za ta bayar da damar ginin layin dogon mai nisan kilomita 500 da zai taimaka wajen aikin kwasar karafa tan miliyan 35 duk shekara cikin shekaru 10 masu zuwa.

Sai dai kasashen biyu ka iya fuskantar tirjiya daga kotu wadda yanzu haka ke shirin zama don shari’a kan karar ta Sundance Resources da ke aikin aikin zai haifar masa asara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.