Ma’aikatan layin dogo sun shiga zulumi saboda hare-haren‘yan bindiga
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:17
Ma’aikatan layin dogo a Najeriya sun bayyana fargaba sakamakon yadda ‘yan bindiga suka fara karkata akalar hare-harensu kan wadanda ke amfani da jiragen kasa domin yin tafiye-tafiye.
Wannan fargaba, ta fito fili ne biyo bayan harin da ‘yan bindigar suka kai a jihar Edo har ma suka yi awun gaba da mutane akalla 30, yayin da a watan maris na shekarar da ta gabata aka yi garkuwa da fasinjoji masu tarin yawa a hanyar Kaduna zuwa Abuja.
A game da wannan farga ce, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Comrade Innocent Luka Ajiji, shugaban kungiyar ma’aikatan layin dogo a Najeriya, ga kuma zantawarsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu