Isa ga babban shafi

China ta gargadi Birtaniya da Amurka kan yarjejeniyarsu da Australia

China ta yi gargadin cewa, kasashen Australia da Birtaniya da Amurka na ratsa wata gurguwar hanya mai cike da hatsari bayan da suka kaddamar da yarjejeniyar cinikayyar jiragen karkashin teku masu amfani da makamashin nukiliya. 

Shugaba Joe Biden na Amurka da Firaminista Anthony Albanese na Australia da kuma Rishi Sunak na Birtaniya yayin jawabi kan yarjejeniyar da suka kulla tsakaninsu kan cinikayyar jiragen ruwa masu nukiliya da aka fi sani da AUKUS.
Shugaba Joe Biden na Amurka da Firaminista Anthony Albanese na Australia da kuma Rishi Sunak na Birtaniya yayin jawabi kan yarjejeniyar da suka kulla tsakaninsu kan cinikayyar jiragen ruwa masu nukiliya da aka fi sani da AUKUS. REUTERS - LEAH MILLIS
Talla

A jiya Litinin ne, Australia ta bayyana cewa za ta sayi jiragen karkashin tekun masu amfani da makamashin nukiliya har guda biyar, sannan ta sake gina wani sabon samfuri na irin wannan jirgin tare da hadin guiwar Amurka da Birtaniya karkashin wani shiri na habbaka karfin kasashen yamma a sassan yankin kasashen Asia da Pacific a daidai lokacin da China ke ci gaba zare musu ido. 

Shugaban Amurka Joe Biden ya jaddada cewa, Australia wadda ta shiga yarjejeniyar hadakar da  Washington da London da aka fi sani da AUKUS watanni 18 da suka gabata, ba za ta mallaki makamin nukiliya ba. 

Sai dai fa, mallakar jirgin karkashin tekun mai amfani da makamashin nukiliya, za ta sanya Australia a jerin manyan kasasahen duniya da kuma na gaba-gaba a yunkurin Amurka wajen dakile China daga fadada karfin sojinta. 

Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen China, Wang Wenbin ya ce, sanarwar hadin-guiwar da Australia da Amurka da Birtaniya suka fitar, na nuni da cewa, kasashen uku, sun yi watsi da muradun kasashen duniya domin cimma burinsu na kashin kansa, abin da ya kira gurguwar hanya kuma mai cike da hatsari. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.