Isa ga babban shafi
Australia-Jirgin Yaki

Australia ta karfafa sojinta da jirage masu nukiliya

A hukumance, Australia ta kaddamar da wani gagarumin shirin karfafa sojojinta da jiragen yakin karkashin teku masu dauke da nukiliya, karkashin wata sabuwar alakar tsaro tsakaninta da Birtaniya da Amurka.

Australia ta karfafa sojinta da manyan jiragen yakin karkashin teku
Australia ta karfafa sojinta da manyan jiragen yakin karkashin teku © AP / Petty Officer 1st Class Michael B. Zingaro
Talla

Ministan Tsaron Australia Peter Dutton tare da manyan jami’an diflomasiyar Amurka da Birtaniya sun rattaba hannu kan wata yarjejejniya da ke bada damar musayar bayanan sirri tsakanin kasashen uku.

A karo na farko kenan da kasashen suka sanya hannu a bainal jama’a kan irin wannan fasaha tun bayan da suka sanar da kafa sabuwar alakar tsaro a cikin watan Satumba  da zummar tunkarar duk wata barazana a Pacific, yankin da China da Amurka ke takun-saka.

Jim kadan da sanya hannu kan yarjejeniyar, Ministan Tsaron na Australia ya ce,  hakan zai ba su damar kammala nazari na tswon watanni 18 game da sayo jiragen yakin karkashin teku.

Gabanin sanya hannu kan yarjejeniyar ta AUKUS, shugaban Amurka Joe Biden ya ce, hakan zai inganta alakar tsaron kasashen uku.

A dalilin yarjejeniyar dai, yanzu haka Autsralia za ta samu kololuwar bunkasa da jiragen yakin karkashin teku masu dauke da nukiliya wandanda kuma za su iya tafiyar aikin soji na dogon zango, baya ga musayar bayanan sirri da kuma karfin zirga-zirga a can karkashin ruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.