Isa ga babban shafi
UN

Majalisar Dinkin Duniya Za Ta Kawar Da Fatara Cikin Shekaru 15

Paparoma Francis da ya halarci taron Majalisar Dinkin Duniya yau, ya yi marhabin da shirin da shugabannin kasashen duniya suka bullo dashi na kawar da fatara a kasashen duniya nan da shekaru 15 masu zuwa.

Paparoma Francis na jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya
Paparoma Francis na jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya REUTERS/Andrew Kelly
Talla

Paparoma Francis wanda yake jawabi a zauren majalisar dake New York ya ce wannan na nuna cewa akwai alamun gaba za ta yi kyau, kodashike tun ba'a kai koina ba wasu dake kushe shirin na ganin zance ne kawai.

Karkashin sabon tsarin dai akwai manufofi 17 da suka shafi ayyuka 169 domin kaiga kawar da fatara a fadin duniya, da samar da wadataccen kiwon lafiya, ilmi da magance dumamar yanayi,  da za su ci kudi Dollan Amirka kusan tiriliyan biyar, duk shekara har ya zuwa shekara ta 2030, wato shekaru 15 masu zuwa.

Sabon tsarin zai maye gulbin maradun karni da ake kawo karshensa wannan shekaran.
Babban Sakataren MDD Ban Kimoon ya bayyana sabon tsarin a matsayin ayyukan da za'ayi wa jama'a da duniya, kuma ana bukatar goyon bayan kowa.

Taron na kwanaki uku da aka fara yau,wasu shugabannin kasashen duniya zasu yi magana gameda tsarin su don kaiga nasarar kawar da fatara karkashin sabbin manufofin MDD.

Cikinsu akwai Shugaban Gwamnatin Jamus  Uwargida Angela Merkel, Fira Ministan Indiya Narendra Modi da kuma Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.