Isa ga babban shafi
Italiya

Bakin-Haure 800 suka mutu a teku-MDD

Majalisar Dinkin Duniya tace bakin haure 800 suka mutu lokacin da jirgin ruwan da suke ciki ya nitse a kusa da gabar ruwan kasar Libya ranar lahadi. Mai Magana da yawun hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Carlotta Sami, tace binciken da suka gudanar da tattaunawa da wadanda suka tsira daga hatsarin ya tabbatar musu da adadin.

Bakin haure da ke kokarin tsallakawa zuwa Turai
Bakin haure da ke kokarin tsallakawa zuwa Turai Reuters
Talla

Hukumomin kasar Italia sun sanar da kama mutane biyu da ake zargin cewar su ke fataucin ‘yan ci-ranin don tsallakawa da su Turai.

Cikin wadanda suka tsira da rayukan su sun hada da Yan kasashen Mali da Gambia da Senegal da Somalia da Eritrea da Bangladesh.

A cikin makon jiya kawai, hukumomin Italiya sun ce sun ceto rayukan bakin bakin haure sama da 11,000, wadanda ke kokarin tsallakawa zuwa Turai.

Hukumomin sun ce a bana adadin bakin hauren da ke kokarin shiga Turai zai zarce na bara inda mutane 170, 000 suka tsallaka.

Wannan kuma na zuwa ne a yayin da hukumomin Turai ke shirin daukar matakai domin magance matsalar kwararan bakin hauren.

Babbar Jami’ar Diflomasiyar Turai Federica Mogherini tace sun fito da wasu matakai 10 domin magance matsalar kwararar bakin haure da ke ci gaba da mutuwa a tekun Italiya.

Jami’ar tace a yanzu ba su da zabi illa su gaggauta daukar mataki game da matsalar bakin hauren

Kungiyar Kasashen Turai ta amince da daukar mataki ne a wani taron Ministocin harakokin waje da na cikin gida da suka gudanar a Luxemburg inda suka tattauna matsalar bakin hauren.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.