Ba ma yaki da Islama-Obama
Shugaban Kasar Amurka Barack Obama ya bukaci shugabanin kasashen Yammacin duniya da na Musulmi su hada kan su dan yaki da masu tsatsauran ra’ayi da wadanda ke fakewa da addinin Islama suna da’awar Jihadi.
Wallafawa ranar:
Yayin da ya ke jawabi wajen taron yaki da tsatsauran ra’ayin da aka gudanar a Washington, shugaba Obama ya ce yan ta’adda da ke batawa Musulunci suna ba su Magana da yawun biliyoyin Musulmin da ke duniya, illa batawa addinin suna.
“Ba ma yaki da addinin Islama, muna yaki ne da mutanen da ke batawa addinin suna” inji Obama.
Wakilan kasashe 60 ne suka halarci taron a Amurka.
Obama ya kuma yi kira a sake daukar matakai domin magance matsalar kungiyoyi irinsu IS da Al Qaeda da ke juyar da tunanin mutane.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu