Mayakan Iraqi sun kashe Ba’amurke a sakon Bidiyo
Kungiyar ‘Yan Tawayen Iraqi da ke fafutukar kafa Daular Islama a kasar sun fitar da wani faifan bidiyo da ke nuna yadda suka kashe wani Dan Jaridan Amurka James Foley da kuma barazanar kashe na biyu muddin Amurka ba ta dakatar da kai harin sama a kasar ba.
Wallafawa ranar:
Kungiyar ta nuna Dan Jarida na biyu Steven Sotloff inda ta ke cewar yanzu haka ransa na hannu shugaba Barack Obama.
Mahaifiyar Foley ta bayyaan shi a matsayin wanda ya bayar da ransa wajen tona asirin mayakan.
Fadar White House ta tabbatar da sahihancin Bidiyon. Kuma a cikin faifan Bidiyon an nuna Dan Jaridar yana karanta sako zuwa ga Amurka da iyalansa.
Bayan James ya kammala karanta sakonsa aka daba masa wuka a wuya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu