Isa ga babban shafi
Ukraine-Rasha

Alaka ta kara yin tsami tsakanin Nato da Rasha

Kungiyar kawancen tsaron ta NATO ko kuma OTAN ta dakatar da huldar tsaro da kasar Rasha saboda karbe ikon Crimea da Rasha ta yi daga Ukraine.

Sakataren kungiyar Nato, Anders Fogh Rusmussen
Sakataren kungiyar Nato, Anders Fogh Rusmussen REUTERS/Francois Lenoir
Talla

Wannan martani ne da kasashen yammaci ke ci gaba da mayarwa Rasha game da karbe yankin crimea da ta yi daga Ukrane a watan jiya.

A taron kungiyar tsaro ta NATO ko Otan a Brussels da ya hada  ministocin harakokin wajen kasashen kawancen kungiyar domin daukar mataki kan Rasha. Sakatare Janar na NATO Anders Fogh Rasmussen ya ce sun dakatar da huldar tsaro da Rasha, kodayake ya ce kofar sulhu a bude take.

Kungiyar ta ce karbe ikon Crimea da Rasha ta yi daga Ukraine babbar barazanar tsaro ce ga kasashen Turai.  Gabanin taron na NATO, Rasmussen ya karyata rahotanni da ke cewae Rasha ta fara janye dakarunta daga kan iyakarta da Ukraine.

To wannan ne dai shi karon farko da Ministocin wajen kasashen na NATO suka gana a Brusssels bayan Rasha ta karbe Crimea, inda suka yi Allah waddai da matakin.

Amma sun amince su sake nazarin kawancensu da Rasha a zaman da za su sake yi a watan Yuni, idan har babu sauyi daga bukatun da suke nema daga Rashan.
Yanzu haka dai Rasha ta datse tallafin Gas da take ba Ukraine, lamarin da ya haifar da tsadar farashin Gas din a cikin Ukraine.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.