Isa ga babban shafi
Syria-MDD

MDD za ta nemi yadda za a kawo karshen rikicn kasar Siriya

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-Moon, ya ce zai yi kira ga kasashen dake da kujerun dindindin a kwamtin tsaron majalisar, da su hada kansu domin magance matsalar rikicin Syria.Ban ya bayyana hakan ne, yayin da wakilan kasashen masu wakilci dindindin a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya suka hadu, domin tattaunawa a kan kudirin da kasar Faransa ta mika na yadda za a lalata makaman Syria masu guba.Sakatare Janar din ya ce akwai bukatar a kawo karshen rikicin, wanda aka kwashe watanni 30 ana yi, domin hakan zai kawo karshen kashe kashen da ake yi da kwararar ‘yan gudun hijra zuwa wasu kasashe.Haka zalika ya ce zai yi wata ganawa ta musamman da ministocin harkokin wajen kasashen da suka hada da Amurka, Rasha, Birtaniya Faransa da China, domin sun tunkari wannan matsalar.A daya baganren kuma, Ban ya ce zai gana a da Sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry da kuma takwaransa na Rasha Sergie Lavrov, duk a wani mataki na kokarin kawo karshen rikicin na Syria.Ana kuma sa ran tattaunawar ta su za ta kasance ne a ranar 28 ga wannan watan na. 

Sakatare Janar na MDD, Ban Ki Moon
Sakatare Janar na MDD, Ban Ki Moon
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.