Isa ga babban shafi
Amurka-Rasha

An soma tattaunawa tsakanin Rasha da Amurka kan Siriya a Geneva.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, da na kasar Rasha Sergy Lavrov sun fara gudanar da muhimmin Taro kan batun kasar Sirya a Geneva. Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da hankalin Duniya ke ci gaba da huskantar kasar ta Siriya bisa barazanar kai harin da kasar Amurka ta yi mata.

John Kerry da Sarggy Laverov
John Kerry da Sarggy Laverov Reuters
Talla

Gabanin wannan taron dai an bayyana cewar da John Kerry na Amurka da Sergy Lavrov na Rasha kowanen su zai je ne da kwararru kan Makami mai Guba, domin tantance binciken da aka gudanar tun daga farko.

Wannan dai na zuwa ne adai dai lokacin da shugaban kasar Syria Bashar al-Assad a wata zantawa da yayi a kafar Talabijin ya bayyana cewar lallai kasar Syriya zata baje Makamanta masu Guba a ga hukumomin kasa-da-kasa, amma fa don albarkacin kasar Rasha da tayi ruwa tsaki a wannan batu.

Shugaba Assad yace ko kusa ba barazanar Amurka ce ta kaisu ga yin hakan ba, harma yana cewar idan Sirya tayi hakan to dole ne ita kuma a sakata cikin mambobin Majalisar haramta amfani da Makaman masu Guba.

Duk wannan dai na faruwa ne a dai dai lokacin da ‘Yan tawayen kasra Syria dai na ci gaba da gwabza fada da Sojin Gwamnati.

A baya dai an rwato ‘yan adawar na bayyana cewar basu amince da batun dakatar da kai harin Amurka a Sirya ba, kawai don ta amince ta mika Makamanta masu Guba ga Majalisar dunkin Duniya.

Amma dai daga cikin ‘yan tawaen da Radio Faransa ya zanta da shi a dlokacin da yake musayar Wuta da Sojin gwamnati, ya bayyana cewar ‘Yan tawaye basu ki amincewa da shirin kasar Rasha ba, wadanda keda wannan ra’ayin ‘yan koren kasashen Turai ne, babu Bakin mu a ciki.

Yace muna bada namu taimako domin lalata Makaman masu Guba, don ana iya amfani da su nan gaba, ya kamata gwamnatocin kasa-da-kasa su san da hakan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.