Isa ga babban shafi
Faransa

An bayyana wadanda suka lashe kyauta Nobel a bangaren Fasaha

An bayyana Bafaranshe Serge Haroche, da dan kasar Amurka David Wineland, a matsayin wadanda suka lashe kyautar Nobel, bangaren fasaha. An baiwa mutanen biyu kyatar ne saboda binciken da suka yi, kan mafin kankantar halittar da suka gano, wadda kuma za ta iya bude kofar bincike mai zurfi kan ma’urorin masu kwakwalwa wato Computers, da ke da mutukar sauri wajen gudanar da ayyuka.Binciken nasu, ya kuma taimaka wajen hada agogon da bashi da matsala wajen bayyana ainihin lokaci, da nan gaba zai zama wanda za a rinka amfani da shi a ko’ina a duniya, ba tare da tararradin canza lokaci ba.Binciken nasu ya taimaka gaya a harkar kimiyya da fasaha, amma sai dai mutane da dama basu fahimce shi ba. 

Taron manema labarun da aka bayana wadanda suka lashe kyautar Nobel a birni Stockholm
Taron manema labarun da aka bayana wadanda suka lashe kyautar Nobel a birni Stockholm Reuters/Bertil Enevag Ericson/Scanpix
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.