Isa ga babban shafi
Birtaniya

Gurdon da Yamanaka sun lashe kyautar Nobel ta Duniya

A yau Litinin aka ba Dan kasar Japan, Shinya Yamanaka da Dan kasar Birtaniya, John Gurdon kyautar Nobel ta Duniya saboda ayyukansu da su ke gudanarwa na bincike akan kwayar halitta, wanda wannan bincike nasu ya kara nuna yiwuwar samun lafiya ga mutane da cututtuka su ka kayar a duk fadin duniya. Gurdon da Yamakana sun gano cewa za a iya mayar da kwayar halittar babban mutum zuwa ta jariri ta hanyar yin dashe, wanda haka ya kara bude idanu wajen gane yadda kwayar halittar Bil Adama ta ke. 

Shinya Yamanaka (Hagu) da John Gurdon (Dama)
Shinya Yamanaka (Hagu) da John Gurdon (Dama) REUTERS/Kyodo
Talla

“Wannan bincike nasu ya kara mana fahimta akan yadda kwayar halittar Bil Adama ta ke gudana, wanda hakan zai ba da damar kara yin bincike akan yadda cututtuka da kuma samar da magungunansu ya ke” inji daya daga cikin Alkalan da ke ba da kyautar.

Gurdon, wanda aka haifa a shekarar 1933, ya nuna farin cikinsa da wanna kyauta da kuma mamakinsa, a yayin da shi kuma Yamanaka, Farfesa ne a Jami’ar Oxford, kuma yana da shekaru 50 a duniya.

A watan Disambar bana ne ake sa ran za a basu kyautukansu na kudi Dalar Amurka Miliyan 1.2, a birnin Stockholm.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.