Isa ga babban shafi
Amurka

Obama ya yi Allah wadai da harin Libya

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama, ya yi Allah wadai da harin da aka kai kan ofishin jakadancin Amurka da ke Libya, wanda kuma ya yi sandiyar mutuwar mutane hudu, cikinsu harda jakadan Amurka. 

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama REUTERS/Jim Young
Talla

Sai dai Obama, ya dauki alwashin cewa harin bazai bata dangatakar da ke tsakanin kasashen biyu ba.

A wani jawabi da Obama ya fitar a fadar White House, shugaban ya yi bayanan ban kwana ga jakadan, mai suna Chris Stevens, da sauran ma’aikatansa da abin ya rutsa da su.

Sai dai Obama a jawabin na sa, ya nuna cewa, kada a dauki harin a matsayin ra’ayin dukkanin ‘Yan kasar ta Libya, inda ya kara da cewa wasu ‘Yan kasar a lokacin hambarar da gwamnatin Ghaddafi sun kaucewa abkawa ofishin jakadancin na Amurka.

“Kasar Amurka na Allah wadai da wannan hari, wanda mai ban tsoro ne,” inji Obama a lokacin da ya ke bayanin.

Ya kuma kara da cewa “kada a ji wata-wata, za mu cigaba da aiki da gwamnatin Libya don mu ga an gurfanar da wadanda su ka aikata wannan aika-aika.”

Musabbabn harin dai ya biyo bayan fitowar wani fim da wani Ba Amurke ya hada inda aka nuna Musulmai a matsayin marasa tarbiya kuma masu yawan fadace –fadace, har ila yau a ka kuma muzgunawa Annabi Muhammad S.A.W. a cikinsa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.