Isa ga babban shafi

Korea ta arewa ta yi gwajin harba makaman atilari 200 zuwa Korea ta kudu

Korea ta arewa ta harba wasu makaman atilari fiye da 200 zuwa cikin ruwa gab da iyakar kasar da Korea ta kudu da kuma wasu tsibirai da ke karkashin ikon Seoul matakin da kasar ta bayyana da takalar fada.

Shugaba Kim yayin kallon gwajin wani makami da Korea ta arewa ta harba.
Shugaba Kim yayin kallon gwajin wani makami da Korea ta arewa ta harba. AP - 朝鮮通信社
Talla

Tuni dai hare-haren na Korea ta arewa ya tilasta kwashe al’ummar tsibirin Yeonpyeong da Baengnyeaong na Korea ta kudu a wani yanayi da Seoul ba ta bayyana dalilin daukar matakin ba.

Ma’aikatar tsaron Korea ta kudun ta ce babu ko mutum guda da ya jikkata sanadiyyar gwajin hare-haren makaman na atileri da makwabciyartata ta gudanar a safiyar yau Juma’a.

Kakakin ma’aikatar tsaron Korea ta kudun Lee Sung-joon ya bayyana gwajin na Korea ta arewa a matsayin takalar fada, lura da yadda makaman suka shigo har yankunan da ke karkashin Seoul.

Cikin jawabin nasa ya yi gargadin cewa wajibi ne Korea ta arewa ta dauki alhakin duk wani rikici da ka iya biyo bayan gwaje-gwajen makaman nata, haka zalika dole su dakatar da makamancin gwajin cikin gaggawa.

Sanarwar da ma’aikatar tsaron Korea ta kudun ta fitar ta bayyana cewa yanzu haka su na nazarta gwaje-gwajen tare da hadin gwiwar Amurka kuma za su dauki matakan da suka dace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.