Isa ga babban shafi

Korea ta Arewa ta harba wasu makamai masu linzami a cikin tekun

Koriya ta Arewa ta harba  wasu makamai masu linzami a cikin tekun a yau   Asabar tsakanin yankin Koriya da China. An harba makamin ne a yau asabar da misalin karfe 4 na safe agogon kasar.

Korea ta Arewa tayi gwajin makamai masu linzami.
Korea ta Arewa tayi gwajin makamai masu linzami. REUTERS
Talla

Harba makami mai linzami na baya-bayan nan ya zo ne a daidai lokacin da wani sojan Amurka, Travis King, ya shiga Korea ta Arewa daga kudancin kasar a ranar Talata, kuma mai yiyuwa ne hukumomi na tsare da shi a can, a cewar rundunar sojin Amurka.

Sojan wanda ke zaman gidan yari a Korea ta Kudu bisa laifin kai hari, dole ne ya koma Amurka domin ya fuskanci kotu.

Ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta yi yunkurin tuntubar sojojin Korea ta Arewa domin jin halin da sojin ke ciki amma ba ta samu amsa ba, in ji kakakin ma'aikatar harakokin wajen Amurka Matt Miller ranar Alhamis.

Makami da Korea ta Area ta cilla
Makami da Korea ta Area ta cilla AP - Ahn Young-joon

 

 

Tun a shekarar 2006 ne Korea ta Arewa ke fuskantar takunkumin kasa da kasa, wanda aka kara sau uku a shekarar 2017.

Matakan da kwamitin sulhun ya dauka a shekarar baki daya domin tilastawa Pyongyang katse shirye-shiryenta na makaman nukiliya da na ballistic musamman takaita shigo da mai daga Koriya ta Arewa.

A cewar wata wasika da kamfanin dillancin labaran AFP ya fitar a ranar Juma'a, Amurka, Tarayyar Turai, Koriya ta Kudu da sauran kasashe sun bukaci taimakon kasar China don hana Korea ta Arewa keta takunkumin mai na Majalisar Dinkin Duniya ta hanyar amfani da yankin ruwan China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.