Isa ga babban shafi

Korea ta Arewa ta gargadi kasashen Amurka da Korea ta kudu

Korea ta Arewa a yau lahadi  ta bayyana cewa ta harba makami mai linzami mai cin dogon zango a jiya asabar a matsayin gargadi ga Washington da Korea ta Kudu , tare da nuna karfin ta na tunkarar duk wata barrazana daga gare su.

Makami mai cin dogon zango na kasar Korea ta Arewa
Makami mai cin dogon zango na kasar Korea ta Arewa © KCNA/UPI/Shutterstock/SIPA
Talla

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya ba da umarnin kaddamar da atisayen ba-zata daga ranar juma'a zuwa  ranar asabar. Korea ta Arewa ta harba makami mai linzami kirar Hwasong-15 daga filin tashi da saukar jiragen sama na Pyongyang.

 Makamin  ya yi tafiya na tsawon mintuna 66 kafin ya faɗo a yankin tattalin arziki na musamman (EEZ) wanda, kwararru ke hasashen cewa zai iya kaiwa ga nahiyar Amurka.

Shugaban Korea ta kudu Yoon Suk Yeol, a martanin da ya mayar, ya nemi karfafa hadin gwiwa da Amurka, babbar kawarsa a fannin tsaro, inda ya yi alkawarin kara atisayen soji na hadin gwiwa, da kuma inganta tayin da Washington ta yi na fadada matakan dakile ta, musamman ta hanyar nukiliya.

A ranar Lahadin da ta gabata, mai magana da yawun Pyongyang, kuma 'yar uwar shugabanta, Kim Yo Jong, ta ce wadannan matakan da Seoul da Washington suka dauka ne ke haifar da barazana a kodayaushe a yankin da kuma tabarbarewar zaman lafiyarta, a cewar KCNA.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.