Isa ga babban shafi

Karon farko cikin shekaru 22 Korea ta Arewa ta yi taro da 'yan jaridar kasar

Gwamnatin Korea ta arewa ta kira ‘yan jaridar kasar zuwa taron manema labaran da ta shirya karon farko cikin shekaru 22 dai dai lokacin da kasar ke fadada shirin nukiliyarta duk da barazanar karancin abincin da kasar ke fama da shi.

Shugaba Kim Jong-un na Korea ta Arewa.
Shugaba Kim Jong-un na Korea ta Arewa. AP
Talla

Kamfanin dillancin labaran Korea ta Arewa ta ruwaito cewa taron manema labaran irinsa na farko tun shekarar 2001 ya nemi shawarwarun ‘yan jaridun wajen bunkasa shirye-shiryen shugaba Kim Jong Un don ciyar da kasar gaba.

Korea ta Arewa wadda iyalan gidan kim ke mulka fiye da shekaru 70 ita ce kasa ta farko mafi take hakkin ‘yan jaridu da kuma tauye hakkin fadar albarkacin baki.

Taron manema labaran na birnin Pyongyang da ya gudana a ranakun litinin da talata na zuwa ne a dai dai lokacin da kebantacciyar kasar ke fuskantar manyan manyan kalubale masu alaka da karancin abinci.

Karon farko kenan karkashin mulkin Kim da ake gudanar da irin wannan taro, shugaban da ya fara jagorantar Korea ta Arewan a shekarar 2011 ya ke kuma karfafa sashen makamin nukiliyarta ba tare da la’akarin jerin manyan takunkuman da ake ci gaba da kakabawa kasar da kuma mayar da ita saniyar ware ba.

A bara ne shugaba Kim Jong Un ya sanar da aniyar komawa kan turbarsa da mallakar manyan makaman nukiliya yayin da ya umarci sojojinsa su zauna cikin shirin yaki na gaske.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.