Isa ga babban shafi
SYRIA

Bashar Assad ba zai sauka daga kujerar shugabanci Syria ba

Gwamnatin Syria, ta ce makomar shugaban kasar Bashar Assad, ba ya daga cikin abubuwan da za a tattaunawa a taron sulhun da za a fara ranar litinin mai zuwa karkashin inuwar MDD a birnin Geneva.

Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad
Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad REUTERS
Talla

Ministan harkokin wajen kasar ta Syria Walid Mu’allem, wanda ke gabatar da taron manema labarai a birnin Damascus a wannan asabar, ya ce ba su da niyyar tattaunawa da duk wanda zai diga ayar tambaya a game da makomar kujerar shugabanci ta Bashar Assad.

Rahotanni daga birnin Geneva dai na cewa, ayarin farko na ‘yan adawar wadanda ke da babbar cibiyarsu a birnin Riyad, ya isa a Geneva domin tattaunawar sulhun da za a fara a jibi litinin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.