Isa ga babban shafi
Syria-MDD-Rasha-Saudiya

Bangarorin dake rikici da juna a Syria na sokar Junan su

Bangarorin da ke rikici a kasar Syria sun zargi junan su da karya yarjejeniyar tsagaita wutar da aka kulla a karon farko bayan kwashe shekaru 5 ana zub da jini a kasar.

Yankin Daech dake Syria
Yankin Daech dake Syria REUTERS/Stringer
Talla

Babbar kungiyar ‘yan tawayen kasar ta bayyana samun ci gaba a shirin tsagaita wutar, sai dai ta gabatar da korafi gaban Majalisar Dinkin Duniya da wasu gwamnatocin kasashe kan abinda ta kira sabawa yarjejeniyar da bangaren gwamnati da sojojin Rasha suka yi.

Salem al Meslet, mai magana da yawun bangaren da ke tattaunawa a Saudi Arabia yace an samu karya yarjejeniyar nan da can, amma hakan bai hana samun nasara ba.

Jami’in ya ce ‘yan adawar na fatar ganin yarjejeniyar ta dore ta har abada.

A bangare daya kuma Saudi Arabia ta zargi Russia da sojojin Bashar al Assad da kai hare haren, sai dai Russia ta zargi ‘yan tawayen Syria ne da kai harin.

Kungiyoyin agaji na son yin amfani da tsagaita wutar wajen raba kayan agaji a sassan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.