Isa ga babban shafi
Japan

Shekaru 70 da kawo karshan yakin duniya na 2 a Japan

Yau Assabar kasar Japan ke gudanar da bikin cika shekaru 70 da kawo karshen yakin duniya na 2, sai dai kuma ta fuskanci kau-kausar suka daga kasashen dake magwabtaka da ita wato China da Korea ta kudu.

Firiya Ministan Japan Shinzo Abe
Firiya Ministan Japan Shinzo Abe Reuters/路透社
Talla

Kasashen Biyu sun Soki Jawabin da Firayi ministan Japan Shinzo Abe ya gabatar na neman afuwa a game da farmakin da Kasarsa ta kaddamar a baya.

Abe dai ya nuna nadama ne kan abubuwan da Japan ta aikata, tare da bukatar sake kulla kyawawa dangantaka tsakaninta da kasashen da suka sabawa.

Kasar Amurka dai ta bayyana gamsuwarta da jawaban Shinzo Abe, inda ta cacaki China kan rashin nuna nadamarta.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.